Zeenat Zakzaky ta rubuta budaddiyar wasika ga Buhari

Zeenat Zakzaky ta rubuta budaddiyar wasika ga Buhari

Zeenat ta kasance matar shugaban musulman Shi’a na Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ta runbuto budaddiyar wasiga ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sakamakon wani karo ya afku tsakanin yan Shi’a da hukumar sojin Najeriya, ma’auratan biyu na tsare bisa ga umurnin shugaban kasa, duk da cewan kotu ta bayar da umurni a sake su.

Zeenat ta rubuto wani wasika dauke da dukkan abubuwan da ya faru tun daga gwamnatin Jonathan har zuwa gwamnati mai ci.

Ga wasikar kamar haka:

Ya kai shugaban kasa,Ina gaishe ka yayinda kake gutu a birnin Landan. Gaisuwata da fatan ailkhairi gare ka da masoyanka dake kula da kai a lokacin da kake bukatar hakan. Ina roka maka gafarar Allah a kan ka.

Ranka ya dade, shin ka tuna watan Yuli na shekarar 2014? Na tabbata ka tuna abubuwan bakin ciki a watan Yuli 2014. Wata ne da kaddara ya hada mu a al’amarin bakin ciki da rayuwa.Yuli 2014 ya kasance watan da Najeriya ta daga sakamakon yunkuri da akayi na daukar ranka a tashin bam da yayi sanadiyan mutuwar kusan mutane dari da basu san hawa basu san sauka ba.

Wannan watan ya kasance lokaci da Allah yayi maka aikin gafara ya cece ka. Watan Yuli 2014 ya kuma kasance watan da hukumar sojin Najeriya karkashin shugaban kasa Goodluck Jonathan suka kashe masi ‘ya’yana guda uku a cikin musulmai 35 dake gudanar da hakkinsu na taruwa. Kaddara ta hada mu a wannan watan yayinda yan Najeriya suka bayyana cewa bazasu yarda ba.

Gwamnan jihar Kaduna mai ci a yanzu, Nasir el-Rufai, ya mika ta’aziyyarsa ga mijina.

Zeenat Zakzaky ta rubuta budaddiyar wasika ga Buhari

Category: Latest News;
;